Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An rantsar da sabon shugaban kasar Faransa

Sabon shugaban kasar Faransa, François Hollande, ya yi kira da a samu wata sabuwar mafita ga Turai. Yayin da ya ke jawabi bayan rantsar da shi, Mista Hollande ya ce zai gabatar da wata shawara a gaban Tarayyar Turai wacce za ta tallata bunkasar tattalin arziki, ba kawai rage yawan bashi ba.