Kabilun birnin Landan cikin hotuna

Landan na cikin biranen duniya da suka fi tattaro mutane mabambanta kuma daya daga cikin birane kalilan inda ake marhabin da bambance-bambance.

Tsage-tsage
Bayanan hoto,

Tsage-tsage: A 'yan shekarun da suka gabata tsage-tsagen jiki sun zama abin kwalliya a tsakanin mutane masu dimbin yawa wadanda ke kallon zanen jiki a matsayin wata hanya ta fahimtar rayuwa.

Bayanan hoto,

Hawan Feda: Kekuna ba ababen hawa kadai ba ne a Landan. Kekunan Vintage Bikes da BMX wadansu kabilun Landan, wadanda suka yi tarayya a kan kaunar kekuna, suke amfani da su.

Bayanan hoto,

'Yan Birni: an san ma'aikatan da ke gundumar kasuwanci da sanya kwat masu tsada da kuma tafiyar kasaita. Da an ga wadannan 'Yan Birni, masu zuba jari, da ma'aikatan banki, da ma'aikatan kasuwar hadahadar hannayen jari, za a ga tasirin kudi.

Bayanan hoto,

Kawa: Landan na cikin biranen duniya da suka shahara wajen dinke-dinke, kuma ba sai mutum ya je inda ake baje kolinsu ba in yana so yana ga samfur. A tituna da gidajen rawa na birnin ma mutane su kan nuna adonsu.

Bayanan hoto,

Makadan Rock: Harkar kade-kade da wake-wake a Landan tana cikin wadanda suka fi bunkasa a duniya. Daruruwan mawaka da makada kan zo Landan suna neman wata dama a wuraren bukukuwan kade-kade da raye-raye da dama. A wannan hoton ana iya ganin biyu daga cikin mambobin wata kungiyar makadan Rock wadanda suka zo Landan daga arewacin Ingila.

Bayanan hoto,

Amarori: mutane daban-daban wadanda suka hadu a kan sha'awar kade-kade da wake-wake da kuma bukukuwan kan titi. Landan matattara ce ta irin wadannan masu sheke-aya saboda yawaitar bukukuwa.

Bayanan hoto,

Punk: a shekarun 1980 wadannan mutanen ruwan dare ne a titunan Landan, amma yanzu sun kusa zama tarihi. A yanzu a mashaya kalilan ne kawai ake ganinsu da gashinsu a tsaitsaye: alamar bijirewa.

Bayanan hoto,

Tsohuwar zuma: Saboda tsananin kawazucin zamanin da, wadannan mutane ke yunkurin maido da bara bana ta hanyar suturunsu da kuma raye-rayen da can.

Bayanan hoto,

Hip hop: a da bakaken fata ake alakantawa da hip hop, amma yanzu ya zama gidan kowa akwai a tsakanin 'yan birni. Hulunan wasan baseball, da takalma 'canvas', da dirkadirkan riguna su ne kashin bayan wannan salo.