Hotunan Gaddafi da ba a taba gani ba

A shekarar 1977, shugaban Libya ya kaddamar da juyin juya halin al'umma inda ya kafa kwamitocin juyin juya halin.

Gaddafi na karatu
Bayanan hoto,

Ajiyayyun hotuna daga Libya na musamman, tun daga zamanin sarki Idris al-sanusi zuwa marigayi shugaba Muammar Gaddafi, za a yi baje kolin su a wannan mako, cikin taron baje kolin hotunan da za a yi a London. Wannan hoton na nuna hoton matashin sojan da ya zamanto jagoran juyin mulki, ya na hutawa da abokansa a hamada, shekaru bayan da ya yi wa sarkin juyin mulki.

Bayanan hoto,

Sarki Idris ya jagoranci Libya daga shekarar 1951 bayan da ta samu 'yancin kai. Wannan hoton na dauke da rubutun hannu ne da aka yi tun a ranar 11 ga watan Maris na 1965 zuwa sarkin Morocco,Sarki Hassan na biyu,wanda ke nufin,''domin tunawa da 'yan uwantaka''.Shekaru hudu bayan nan Gaddafi ya hambare shi daga gadon sarauta kuma ya kawo karshen zaman gudun hijirarsa a Masar..

Bayanan hoto,

A lokacin yakin duniya na biyu, sarkin ya goyi bayan Birtaniya inda ya juyawa turawan Italiya da suka mulki kasar ta Libya baya. Wannan hoton da aka dauka jim kadan bayan samun yancin kan kasar, na nuna Sarauniya Elizabeth ta biyu lokacin ziyarar ta a Tobruk, inda Birtaniya ta ke da sansanin sojin sama wanda Gaddafi ya rufe a shekarar 1970. Sabon shugaban na son gyara abin da ya ke ganin miyagun abubuwan ne mulkin mallakar turawa.

Bayanan hoto,

Wannan hoton lokacin karbe ma'aikatar hakar mai ne aka maida ita mallakar kasar ta Libya da kuma sake yarjejeniya da kamfunan hakar mai - inda ya yi musu barazanar rufe aikinsu idan ba su amince da ka'idojinsa ba.Gaddafi mai sha'awar shugaban Masar ne na farko da ta sami mulkin kai Gamal Abdul Nasser, wanda ake gani a nan afilin wasan Benghazi a watan Disamba 1969.

Bayanan hoto,

A tsawon mulkinsa na shekaru 42, Gaddafi ya na da manufofin hulda da kasashen waje masu sarkakiya.Da farko dai ya na bin manufofin kungiyar hadin kan Larabawa. A wannan hoton, mutane ne su ka mamaye Gaddafi da shugaban Sudan da na Masar a Tripoli a shekarar 1969.

Bayanan hoto,

Gaddafi ya yi yunkurin hadewa da sauran kasashen Larabawa, ciki har da Masar da Syria da Tunisia, to amma hakan ba ta yuwu ba da dukkanin kasashen . A shekarun 1990, ya juya akalarsa ga kasashen Afirka dake yamma da Hamada, inda ya fahimci cewa arzikin kasar sa zai kara ba shi tasiri.

Bayanan hoto,

Shugaba Gaddafi ya yi kaurin suna ga kasashen yammacin duniya saboda goyon bayansa ga dakarun Jamhuriyar Ireland.kuma ya na da kyakkyawar alaka da kungiyar fafutukar neman 'yancin Palasdinawa ta PLO, a lokacinda Yasser Arafat,(wanda ake gani a hoton nan lokacin da ya ziyarci Libya) ke yi mata jagora.

Bayanan hoto,

To sai dai, dangantakarsa da shugabannin kasashe kan hau ta sauka. A nan Gaddafi ne da shugaban tarayyar Soviet Leonid Brezhnev rike da hannun juna a shekarar 1981.

Bayanan hoto,

A shekarar 1977, shugaban Libya ya kaddamar da juyin juya halin alumma inda ya kafa kwamitocin juyin juya halin, lokacin da mulkin danniyarsa ya karu. Wannan hoton na nuna inda a ke rataye mutane cikin wannan shekarar a Benghazi, birnin da a ka fara juyin juya halin watan Fabrairun shekarar 2011, kuma har ya kai ga halaka Kanar Gaddafi a watan Oktobar wannan shekarar.

Bayanan hoto,

Darektan kula da taimakon gaggawa na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, Peter Bouckaert ne ya tattara wadannan hotuna na tarihi, wadanda ya samu daga ginin hukumar leken asirin kasar da kuma gidajen Gaddafi da aka lalata a lokacin juyin juya halin Libya.Tim Hetherington da Chris Hondros wadanda dukkanin su suka mutu lokacin da a ka jefa wani bam a Misrata, a bara, su ne su ka sake daukar hotunan daga hotunan na ainahi. Za a yi bikin baje kolin kayan tarihi na Gaddafin ne da a ka yiwa lakabi da, Libya kafin juyin juya halin kasashen larabawa da za a bude a cibiyar bincike ta Slade Research Centre da ke London a ranar 21 ga wannan wata.