Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu: Sabon Ginin Yada Labarai na BBC

Wannan shirin na Taba Kidi Taba Karatu na musamman ne; Sulaiman Ibrahim ya tattauna da Umar Yusuf Karaye a kan yadda aiki ya kasance a Bush House da kuma yadda zai kasance a Sabon Ginin Yada Labarai na BBC. Bayan shekaru tamanin, Sashen BBC mai yada shirye-shirye ga kasashen duniya, ya tashi daga Bush House, ya koma New Broadcasting House.