Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ko yaya azumin bana ya zo muku?

Al'ummar Musulmi a fadin duniya sun fara azumin watan Ramadhan, wanda shi ne wata mafi tsarki ga Musulmi.

Baya ga kasancewarsa watan da aka saukar da Al'Kur'ani mai tsarki, a cikin watan na Ramadan ne kuma Musulmi suka yi imanin cewa Allah Madaukakin Sarki kan yi kididdigar ayyukan bayinsa na shekarar da ta gabata.

Watan kan kuma koya wa Musulmi darussa da dama, ciki har da kame kai da fahimtar irin yanayin da marasa karfi a cikin al'umma ke rayuwa a cikinsa.

Saboda haka ne ma a cikin watan mai tsarki Musulmi kan yawaita ibada da ayyukan alheri, saboda samun dacewa da falalar dake cikinsa; su kan kuma yawaita addu'o'in neman gafara.