Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nonon Uwa na da muhimmanci matuka

Wannan makon ne dai Makon Shayar da Nonon Uwa na Duniya karo na ashirin; an kebe shi ne domin kara fadakarwa a kan muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla har tsawon watanni shida tun daga haihuwa.

Hukumomi na duniya sun bayyana cewa kashi goma sha uku cikin dari ne kawai na jarirai a Nijeriya kan samu shayarwar nonon uwa zalla har na tsawon watanni shidda na farkon rayuwarsu.

Shin a ina matsalar take? Me ya sa wasu iyayen suka ki karbar wannan tsari hannu biyu-biyu?