BBC navigation

Zakarun Olympics daga nahiyar Africa

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 10:31 GMT

Labarai cikin hotuna: 'Yan wasan Afrika a gasar Olympic

 • David Lekuta Rudisha dan kasar Kenya ne a kan gaba
  An kammala gasar Olympics na shekarar 2012 kuma kasashen Afrika na yin nazari kan yadda ta kaya a London. Nahiyar ba ta samu lambobin yabo masu yawa ba a gasar ta London kamar yadda ta samu a Beijing. Amma wasu 'yan wasa daga Afrika mata da maza na cikin wadanda suka nuna bajinta ga duniya. 'Yan wasan sun hada da David Rudisha na kasar Kenya, wanda nasarar da ya samu a tseren mita 800, kafin Nijel Amos dan Boswana da wani dan Kenyar Timothy Kitum ke daga cikin lokuta mafi kayatarwa a gasar ta London.
 • Ezekiel Kemboi na kan gaba a lokacin tseren
  Wani dan Kenya Ezekeil Kemboi ya samu lambar zinare a gasar tsallen badake na mita dubu uku. Yayin da dan uwansa Abel Kiprop Mutai kuma ya samu lambar tagulla.
 • Lambar zinaren da Afrika ta Kudu ta samu a gasar Olympics
  Kasar Afrika ta Kudu ta yi zarra a kasashen nahiyar Afrikan da suka fafata a gasar Olympics, inda ta samu zinare uku, azurfa biyu da tagulla guda. 'Yan wasan ninkaya Cameron Van der Burg (dama) da kuma Chad le Clos dukkansu sun samu lambobin zinare a tseren ninkaya na mita 100. Haka kuma Le Clos ya samu azurfa a wani nau'in ninkaya na mita 100.
 • 'Yan Afrika ta Kudu masu gasar tuka kwale-kwale Sizwe Ndlovu da John Smith da Mathew Brittain da James Thompson
  'Yan Afrika ta Kudu masu gasar tuka kwale-kwale Sizwe Ndlovu da John Smith da Mathew Brittain da kuma James Thompson sun samu lambar zinare a tseren kwale-kwale na mutane hur-hudu.
 • Mariya Savinova da Caster Semenya
  'Yar Afrika ta Kudu Caster Semenya ta samu azurfa a tseren mita 800 na mata. Mariya Savinova 'yar kasar Rasha ce ta dauki lambar zinare. Semenya ta samu komabaya tun bayan komowarta fagen wasa bayan an dakatar da ita na watanni 11. Hakan ya biyo bayan cece-kucen da aka samu game da lashe gasar duniya da ta yi a shekarar 2009 wanda ya sa aka yi mata gwaje-gwaje game da jinsinta.
 • Jepkemoi Cheruiyot 'yar kasar Kenya da Gelete
  'Yar kasar Habasha Meseret Defar ta baiwa 'yar uwarta Tirunesh Dibaba mamaki, inda ta sake karbe kambunta a tseren mita dubu biyar a gasar Olympics. Ta samu lambar da fari a gasar da aka yi a Athens a shekarar 2004. Dibaba wacce ta riga ta samu lambar zinare a tseren mita dubu goma ta zo ta uku bayan 'yar Kenya Vivian Cheruiyot.
 • Tiki Gelana ta kammala gudun famfalaki
  Wata 'yar kasar Habasha da ta haskaka kuma ita ce Tiki Gelena wacce ta lashe gudun famfalaki na mata, yayin da 'yar kasar Kenya Priscah Jeptoo ke biye da ita.
 • Abel Kirui dan Kenya da ya samu azurfa da kuma wanda ya samu zinare
  Haka batun yake a gudun famfalaki na maza, inda 'yan Afrika suka haskaka. Stephen Kiprotich ya samu lambar zinare ga kasarsa ta Uganda wacce rabonta da daukar zinare tun shekarar 1972. Lambobin azurfa da tagulla a gasar dai 'yan kasar Kenya Abel Kirui da Wilson Kipsang ne suka samu.
 • Taoufik Makhloufi dan Algeria ne ya samu lambar zinare
  Dan kasar Algeria Taoufik Makhloufi ne ya lashe tseren mita 1, 500 na maza. Wannan ne karon farko da ya dauki lambar yabo ta duniya a rayuwarsa. Dan Morocco Abdalaati Iguider ne ya samu azurfa a gasar.
 • Oussamu Mellouli
  Dan kasar Tunisia Oussamu Mellouli ne ya zo na farko a wani nau'in gasar ninkaya, inda ya samu lambar yabo a ninkayar kilomita 10 a Hyde Park dake London. Dan shekaru 28 din ya kuma samu lambar tagulla a ninkayar mita 1,500.
 • Anthony Obame a hannun hagu na fafatawa da Carlo Molfetta
  Dan wasan damben Taekwondo Anthony Obame ya kafa tarihi, inda a karo na farko ya samarwa kasarsa Gabon lambar yabo a gasar Olympics. Ya samu lambar azurfa bayan ya sha kaye a hannun Carlo Molfetta dan Italiya.
 • Alaaeldin Abouelkassem da Lei Sheng
  Dan kasar Masar Alaaeldin Abouelkassem ya zama dan Afrika na farko da ya kai wasan na kuda da na kusa da na karshe a wasan takobi a Olympics. Ya samu lambar azurfa yayin da dan kasar Sin Lei Sheng ya lashe gasar.
 • Oscar Pistorius
  Kodayake dan kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius bai samu lambar yabo ba, amma ya kafa tarihi kasancewar sa wanda ba shi da kafa na farko da ya taba fafatawa a tseren masu kafa a gasar Olympics. Dan wasan ya samu lambobin yabo a gasar nakasassu ta paralympic har sau hudu, an yanke masa kafa ne daga daidai guiwa a lokacin da yake jariri. Kuma zai fafata a gasar Paralympics da za a bude a ranar 29 ga watan Agustan shekarar 2012.
 • Hamadou Djibo Issaka
  A karshe sai dan Nijar Hamadou Djibo Issaka wanda aka yi wa lakabi da "Issaka the Otter" a turance. Ya faranta zukatan mutane da dama duk da cewa ya kammala tserensa minti daya bayan abokan gasarsa. Issaka wanda mai kula da lambu ne ya fara samun horo a tukin kwale-kwale watanni uku da suka wuce, kafin fafatawarsa ta farko a Olympics da wani tsohon kwale-kwale.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.