BBC navigation

A Hyderabad, in ba ka dandana haleem ba, ba ka yi bude-baki ba

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:00 GMT

A Hyderabad, in ba ka dandana haleem ba, ba ka yi bude-baki ba

  • Baya ga kasancewarsa watan azumi da ibada, Ramadan lokaci ne na bukukuwa da nishadi a Hyderabad, lokacin da launuka da fitilu kan kawata birnin. Wannan hoton na ginin Charminar ne mai tarihi cike da masu sayayya.
  • Shaharar haleem ta zama ruwan dare a tsakanin al'umma. Wani saurayi da ya dandana haleem ya ce "Da Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba suna kawazucin zuwan Ramadan saboda haleem".
  • Turare ko atar na cikin abubuwan da mutane ke matukar sha'awa a lokacin Ramadan. A bana, za a yi bukukuwan Sallah ne ranar 19 ko 20 ga watan Agusta a India. Masu sayayya suna ta cefanen Sallah wacce za a yi a karshen Ramadan.
  • A lokacin azumin watan Ramadan, bude-bakin mutanen Hyderabad ba ya kammala ba tare da Haleem ba, wani abinci mai kauri kamar talge (ko dan malele) da ke da dadi. Ana yinsa ne da alkama, da shinkafa, da nama, ana kuma tsarma kayan yaji, da busassun 'ya'yan itace da sauran abubuwa. Iraniyawa ne suka kawo haleem birnin Hyderabad mai shekaru 400.
  • Sauran kayayyakin da ake yin haleem da su sun hada da zeera, da shah zeera (wadansu nau'uka na kayan yaji), da dal cheeni, da kebab cheeni, da kajju (kashu), da madara; sannan a biyo bayansu da soyayyiyar albasa, da koren coriander, da kuma ghee (man shanu).
  • Shaharar haleem ta zama hantsi leka gidan kowa. A nan wata 'yar yawon bude-ido ce ba'Amurkiya ke more haleem.
  • Dafa haleem jan aiki ne da ake farawa da dukuduku a kuma kwashe sa'o'i takwas zuwa goma ana yi. Bayan an saka alkama da shinkafa, da nama, ana dafa shi a wani babban kasko, ana daka shi.
  • Bukuwan Ramadan na musamman da ake gudanarwa a Hyderabad sun hada da gasar dafa haleem wacce gidan abinci na Pista House ke shiryawa. A kan baiwa wadanda suka dafa haleem mafi dadi cikin mafi karancin lokaci kyautar kudi.
  • Wata 'yar fim da ke zaune a birnin Hyderabad tana dandana haleem a Sarvi, daya daga cikin wuraren da suka shahara wajen dafa shi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.