BBC navigation

Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi

An sabunta: 21 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 11:40 GMT

Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi

 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  Meles Zenawi ya mamaye siyasar kasar Habasha fiye da shekaru ashirin. A wannan hoton yana halattar taron duniya ne kan tattalin arziki a birnin Davos a watan Janairun 2012.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  Yana halattar biranen kasashen duniya da dama. Anan yana halartar wani taro ne kan batun sauyin yanayi tare da Fira Ministan Burtaniya Gordon Brown a watan Maris na 2010 a London.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  A karkashin jagorancinsa, Habasha ta samu daukaka a idon kasashen duniya. Anan yana isa birnin Denmark domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani kan mutuwar ta sa. Fira Ministan Burtaniya David Cameroon ya ce Mr Meles "na wakiltar Afrika a fagen al'amuran kasashen duniya. Rawar da ya taka wurin bunkasa tattalin arzikin Habasha da fitar da mutane daga kangin talauci, abin koyi ne ga sauran kasashen yankin," a cewarsa.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  Ministan harkokin wajen Habasha Hailemariam Desalegn yana jawabi ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 66 a New York. Hailemariam Desalegn zai jagoranci kasar a matsayin riko sakamakon mutuwar Zenawi.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  A karkashin Mr Zenawi, Habasha ta karfafa matsayinta a yankin. Ya tura sojoji har sau biyu domin su yaki kungiyar Al-Shabab mai alaka da Al-Ka'ida a kasar Somalia mai makwaftaka.
 • Hotuna: Rayuwar Meles Zenawi
  Masu adawa da shi sun zarge shi da cin zarafin 'yan adawa. 'Yan adawa sun gudanar da zanga-zanga lokacin da ya kai ziyara London.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.