Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu: Wani mutum ya ciji miciji har lahira

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Maciji

Wani manomi a kasar Nepal ya ciji maciji har sai da macijin ya mutu, saboda huce haucin sarar da macijin ya yi masa tun da fari.

Kububuwar ta sari Mohammed Salimu wani manomin shinkafa a gonarsa, amma sai da ya je gida ya samo tocila ya lalubo macijiyar kuma ya gartsa mata cizo har ta mutu.

Za ku ji wannan da sauran labaran dake kunshe a cikin shirin Taba Kidi Taba Karatu na wannan makon.