BBC navigation

Babu maza a kauyukan Bukhara

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:45 GMT

Kauyukan da ba maza

 • Kauyukan tsit ka ke ji, yayin da mazauna cikinsu suka ce idan an samu rasuwa da wuya ake samun mazan da za su binne gawar, tun da a gargajiyance ba a san mata da binne gawa ba.
 • Duk wasu ayyuka kama daga zuwa kasuwa, sayen abubuwan masarufi don iyali, kai hatta girbin kayan amfanin gona mata ne ke yi.
 • Tun da duku-duku har zuwa maraice mata ne ke aiki a gonaki, suna rufe fuskokinsu da kyallaye don kare kansu daga kurar dake tashi da kuma zafin rana.
 • Mata na girbin hatsi ta hanyar amfani da jakuna da amalanke.
 • Wasu mata matasa dake aiki a gona ke boye fuskokinsu.
 • Wasu mata sun gaji, suna neman motar da zata dauke su da kayayyakin da suka sayo.
 • Wasu daga cikin matan kauyen suna ayyukan hannu da aka san maza da su, kamar wajen taimakawa mahauta.
 • Mata sun taru a dakin taro don tattauna abubuwan da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum. Dakin taron dai an gina shi ne da kudaden da iyayensu maza da 'ya'yansu da mazajensu suka aiko daga Rasha.
 • Yayin da wasu kuma kan zauna a tsakar gida suna tattauna labarin mazajensu da 'yan uwansu dake kasashen waje.
 • Mata matasa na shirya abinci a dakin girki wanda ke da murhu na gargajiya da kuma abin dafa abinci na zamanin Soviet.
 • Su kan tara kirare a dakin girki, kuma da su ake amfani wajen dafa abinci.
 • Da ganin fuskar wannan mai sayar da burodin, ka san tana cikin kuncin rayuwa a Samarkand.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.