Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Kasuwanci tsakanin kasashen yankin Sahara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata Kasuwa a Najeriya

A makon jiya ne aka gudanar da wani taro a jihar Kano tsakanin gwamnati da 'yan kasuwar jihar da kuma takwarorinsu na jamhuriyar Nijar.

An dai gudanar da taron ne da nufin bunkasa kasuwanci da zuba jari tsakanin bangarorin biyu, da kuma warware wasu matsaloli da suka addabi 'yan kasuwar bangarorin biyu, musamman ma wajen zirga-zirga.

Ministan kula da al'amuran dabbobi na jamhuriyar ta Nijar ne ya jagoranci tawagar kasar, da suka hada da gwamnonin jihar Zindar, da Maradi da Kuma Yamai gami da wasu manyan jami'an gwamnati.

Kuma bisa haka ne wakilin mu a Kano ya hada mana wata tattaunawa ta musamman da wasu mahalarta taron kan kalubalen da ake fuskanta a fannin kasuwanci.