Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda za a magance yawan afkuwar haduran Mota

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hadarin Mota

Wata matsala da ta addabi kasashen Afruka a 'yan shekarun nan ita ce ta yawan aukuwar hadurran mota, abun da ke yin sanadiyyar hallaka dimbin jama' kusan kowacce rana.

Alal misali a Najeriya, da wuya a yi mako guda ba tare da ka ji an yi wani hatsarin mota a kan hanyoyin kasar ba.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ce, mutum miliyan daya da dubu dari uku ne ke mutuwa kowacce shekara a duniya sakamakon hadurran mota kuma WHO tace, matsalar zata cigaba da karuwa.

Koda a kwanakin baya wasu kafofin yada labaru sun ambato ministan lafiya na Najeriya na cewa, kasar ita ce ta biyu a duniya wajen yawan mutuwar mutane sakamakon hatsarin mota, kuma wasu masu harkar kula da kiwon lafiya sun ce, kashi tamanin na masu zuwa asibiti sun je ne da larurorin da suka shafi hatsarin mota.

A watan Agusta mutum Talatin sun mutu sakamakon hatsarin mota a jihar Yobe dake arewacin Najeriya.

Ko a makon nan, mutum Talatin sun mutu sakamakon hatsarin mota a jihar Ogun dake kudancin Najeriya, kuma irin wannan kan faru daga lokaci zuwa lokaci.

Ana dai danganta irin wadannan hadurra ne ga lalacewar hanyoyi da kuma rashin kiyaye ka'idojin tuki da kuma amfani da hanya, da ma matsalar tsaro da kan tilastawa mutane yin tafiye-tafiye cikin hanzari.

Shin ko yaya lamarin yake a yankunan ku? Kuma ta yaya za a shawo kan wannan matsala?

Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna a shirin na yau.