Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Yaki da cin hanci da Rashawa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Shugaban EFCC a Najeriya, Ibrahim Lamurde

A kwanakin baya ne Jami'ar Cambridge dake Ingila ta shirya wani taron karawa juna sani dangane da koyon dabarun yaki da cin hanci da rashawa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen dakile laifukan da suka shafi yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Taron wanda aka gudanar da shi a London, ya sami halarcin wakilan Kasashe sama da 40, inda kowacce kasa ta gabatar da kasida dangane da irin nata dabarun.

Shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da kuma muggan kwayoyi ta majalisar wakilan Najeriya, Jagaba Adams Jagaba na daya daga cikin wakilan da suka halarci taron da jami'ar ta cambridge ta shirya daga Najeriya.

Bayan taron kuma ya kawo ziyara ofishinmu dake London inda Ibrahim Mijinyawa ya tattauna da shi a kan irin abubuwan da zai ce Najeriyar ta koya daga taron.