Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za a kayyade farashin cocoa a Ivory Coast

Yanzu haka, Ivory Coast ce ke samar da akalla sulusi na abin da ake samarwa a duniya. Ke nan duk shekara ta kan samar da cocoan da ake amfani da shi don sarrafa miliyoyin karan cakulet.

Sai dai manoma a kasar, wacce ta fi ko wacce samar da cocoa a duniya, ba dadin rayuwa suke ji ba--tallafin da suke samu daga gwamnati bai taka kara ya karya ba, sannan ga shi suna fama da yawan sauye-sayen farashi a kasuwannin duniya.

Amma gwamnatin kasar ta Ivory Coast za ta bullo da wani sabon tsari na kayyade farashi ga manoman, kamar yadda ake yi a Ghana, kasa ta biyu a samar da cocoa a duniya.