Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Gwamnan Sokoto na Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, shugabanni da sauran jama'a na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda za a warware matsalolin da kasar ke fama da su a yanzu haka.

Daya daga cikin matsalolin sun hada da tabarbarewar sha'anin tsaro, musamman a Arewacin kasar inda kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunna Lid da'awati Wal Jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram ta sha kai hare-haren bam a yankin.

A lokacin wata ziyara da ya kawo mana a ofishin mu na London a kwanan baya, Gwamnan Jahar Sokoto, Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako ya ce hanya mafi a'ala da za a shawo kan matsalar tsaron, ita ce ta tattaunawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram , ba wai yakar su ba.

Hazalika a cikin hirar da Mohammed Kabir Mohammed ya yi da shi, Gwamnan na Sokoto ya tabo sauran batutuwa da suka hada da batun kirkiro da 'yan sandan jihohi da sha'anin kiwon lafiya da ma harkar noma.

Muhammad ya soma ne da tambayar shi ko menene gaskiyar gano man fetur da aka ce an yi a jahar Sokoton?