BBC navigation

Zaman dar- dar tsakanin Syria da Turkiyya

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:50 GMT

Hotuna: Zaman dar-dar tsakanin Syria da Turkiyya

  • Garin Akcakale dake kudancin bakin iyakar Turkiyya, ya sha ruwan bama-bamai daga Syria a ranar Laraba. Abin da ya sa Turkiyya ta maida martani da harbi a kan wasu gurare a Syrian.
  • Wani bam daga cikin wadanda Syrian ta harba Turkiyya ya kashe wata mata da 'ya'yanta uku da kuma wani mutum guda.
  • Turkiyya ta cigaba da harbi da makaman igwa kusa da garin Tall al-Abyad dake bakin iyakar Syria ranar Alhamis. Yayin da ta kara tura karin dakaru Akcakale.
  • Maida martanin da Turkiyya ta yi shi ne karo na farko tun lokacin da aka fara rikicin Syria watanni 18 da suka gabata.
  • An yi jana'izar mutane biyar din da suka mutu a Akcakale.
  • Mazauna garin sun hallara a wajen jana'izar wadanda suka mutun.
  • Wannan mutumin dan uwa ne ga daya daga cikin wadanda suka mutu. Kuma an dauke shi ranga-ranga bayan ya suma a wajen na'izar.
  • Wasu mazauna garin sun yi bore a lokacin da ministan kwadago da jindadin jama'a na Turkiyya ya isa. Abin da aka rubuta a kwalin da wannan mutumin ke dauke da shi, shi ne: 'yan majalisa ya aka yi kuka zo Akcakale, bayan kun juya mana baya.
  • An daura tutar 'yan tawayen Syria a bakin iyakar kasar da garin Akcakale. Gwamnatin Syria ta nemi afuwar Turkiyya, kuma ta dauki alhakin ruwan bama-baman.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.