BBC navigation

Wasu na adawa da batun sa ido a shafukan Intanet

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:44 GMT

Garmaho

Masu rajin tabbatar 'yancin fadar albarkacin baki a shafukan intanet na nuna adawa da wani rahoton majalisar dinkin duniya da ke kiran da a kara sanya ido kan abubuwan da ke gudana a shafukan intanet.

Kallimp4

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Masu rajin tabbatar 'yancin fadar albarkacin baki a shafukan intanet na nuna adawa da wani rahoton majalisar dinkin duniya da ke kiran da a kara sanya ido kan abubuwan da ke gudana a shafukan intanet.

Ofishin majalisar dinkin duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da sauran manyan laifuka ne ya fitar da rahoton da ke nuna cewa intanet ta zama wani makami da 'yan ta'adda ke amfani da shi wajen yada farfagandar su, da kuma samun karin magoya baya.

Sai dai kungiyar ta Open Rights ta yi gargadin cewa, kara karfafa sa ido kan abubuwan da ke gudana a intanet daga hukumomi ka iya barazana ga hakkokin biladama.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.