Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 363 a Najeriya

Ambaliyar ruwa a Najeriya
Image caption Ambaliyar ta bana ita ce mafi muni a shekaru 50

Jami'ai a Najeriya sun ce fiye da mutane miliyan biyu ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a bana.

A cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, wato NEMA, ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dari uku da sittin da uku tun daga wata Yuli.

Ambaliyar, wacce ita ce mafi muni da aka gani a kasar a shekaru hamsin, ta shafi sassa da dama na kasar, musamman yankunan da ke makwabtaka da Kogin Kwara.

Wakilin BBC a Lagos, Will Ross, ya ce yanzu dai ruwan yana janyewa, amma ana faragabar za a samu karancin abinci bayan da wadansu manoma suka yi asarar amfanin gonarsu gaba daya.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton cewa a watan jiya Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ambaliyar wata annoba ce, amma kuma a cewarsa ba ta haddasa matsalar karancin abinci ba.

Wakilin BBC ya ce rashin ingantattun magudanan ruwa a biranen Najeriya kan taimaka wajen haifar da ambaliya idan aka yi ruwa kamar da bakin kwarya.

A wadansu yankunan karkara kuma mutane sun bayyana yadda suka tsorata bayan sun ga kadoji, da macizai, da ma dorinar ruwa a gidajensu da ruwan ya mamaye.