BBC navigation

Waiwaye: 'Yan takarar shugabancin Amurka

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:01 GMT

Waiwaye: 'Yan takarar shugabancin Amurka

 • Jariri Obama a hannun mahaifiyarsa da jariri Romney a hannun mahaifinsa
  Tun kafin su san me ake kira fadar White House... a nan Barack ne yana jariri da mahaifiyarsa, Ann Dunham, a Hawaii, da kuma Mitt yana jariri a hannun mahaifinsa George Romney, wanda ya zama shugaban kamfanin American Motors kuma gwamnan Michigan (hoton gefen hagu: AP)
 • Obama da Romney dauke da kulkin baseball lokacin suna yara
  Ba Amurkancin da ya fi wannan. Obama yana yaro dauke da kulkin wasan baseball a Hawaii, yayin da Romney, lokacin yana dan shekara shida yake shirin dukan kwallon baseball a Detroit (hoton gefen dama: AP)
 • Obama da mahaifin sa, Romney ma da mahaifinsa
  An sanya wa Obama sunan mahaifinsa ne, wani masanin tattalin arziki daga Kenya. Sai dai kuma a galibin rayuwarsa mahaifin bai kasance tareda su ba. A nan suna tare ne yayin wata ziyarar mahaifin wadda ba kasafai ya kan kai musu irinta ba a Hawaii. Romney dan gaban goshin mahaifinsa ne. A wannan hoton ana iya ganinsa da mahaifin nasa jim kadan bayan George Romney ya zama gwamnan Michigan (hotunan biyu: AP)
 • Barack da Michelle Obama, Mitt da Ann Romney
  Bayan kammala karatunsa na lauya a Jami'ar Harvard, Obama ya hadu da Michelle Robinson a wani kamfanin lauyoyi a Chicago. Tun suna makaranta Romney da Ann Davies suka san juna, sun kuma yi ta aikewa juna wasika lokacin da Romney ya tafi aikin mishan na shekaru fiye da biyu a Faransa
 • Auren Obama da auren Romney
  Jim kadan bayan dawowarsa daga Faransa aka daurawa Romney da Ann aure--a lokacin duk su biyun dalibai ne. Obama da Michelle sun yi aure ne a shekarar 1992
 • Obama da Romney
  Obama ya yi aiki a Makarantar Koyon Aikin Lauya a Jami'ar Chicago, kuma a shekarar 1992 ya yi aikin wayar da kan mutane su yi rajistar zabe a Illinois. Romney ya taimaka an kafa kamfanin zuba jari na Bain Capital, kuma ya tsaya takarar Majalisar Dattawa ta Jihar Massachusetts a shekarar 1994, amma ya sha kaye a hannun Ted Kennedy (hotunan biyu: AP)
 • Romney da iyalansa
  Iyali na da muhimmanci a wurin 'yan takarar biyu. Romney da Ann suna da 'ya'ya maza biyar wadanda yanzu duk sun girma, da kuma jikoki 18
 • Obama da iyalansa
  A matsayinsa na shugaban kasa, Obama na da matsattsen jadawali, amma a galibin ranakun mako ya kan yi kokari ya ci abincin dare tare da Michelle da 'ya'yansu biyu mata, Sasha da Malia. Tun bayan Jimmy Carter fiye da shekaru 30 da suka wuce, Barack da Michelle ne farko da suka zauna a White House da yara matasa
 • Obama na karatu, Romney na jawabi
  Obama a shekarar 2004, lokacin da ya zama sabon dan Majalisar Dattawa, yana tilawar jawabin da ya gabatar a wurin Babban Taron Jam'iyyar Democrat na Kasa--jawabin ne ya sa tauraruwarsa ta fara hasakawa a fagen siyasar kasar Amurka. Nasarar da ya yi ta sauya akalar Gasar Olympics ta lokacin sanyi a shekarar 2002 ce ta baiwa Romney kwarin gwiwar shiga takarar gwamnan Massachusetts, zaben da ya lashe (AP/Getty)
 • Obama rike da kwallon kwando, Romney kuma ya daga rigar kungiyar kwallon kwando ta Boston Celtics
  Duka 'yan takarar biyu na sha'awar motsa jiki. Obama na kaunar kwallon kwando an kuma ce ya kware sosai. A nan an baiwa Romney rigar kungiyar kwallon kwando ta Boston Celtics ko da yake ya fi sha'awar shiga wasu wasannin na daban (AFP/AP)
 • Obama na buga wasan golf, Romney na ninkaya a ruwa.
  Me yasa shugabannin kasa ke damuwa da wasan golf? Obama na wannan wasa sosai ko da yake ya kan ce bai iya sosai ba sai dai yana son wasan tare da fitowa don shan iska. Romney ma na son fita waje don shan iska ko kuma bakin ruwa. A nan shi ne ya ke iyo a bakin tafki lokacin da ya je hutu a New Hampshire.
 • Obama na sumbatar Michelle, Romney ma na sumbaci Anna
  Ana ganin masu dakin 'yan takarar biyu a matsayin kashin bayan yakin neman zaben su, dukkannin su sun gudanar da jawaban dake koda mazajen nasu a lokacin gangamin. A matsayinta na Uwargidan Shugaban Kasa, Michelle Obama ta yi suna wajen kula da lafiyar kananan yara, yayinda Ann Romney kuma ke alkawarin kula da mata masu cutar kansar mama da kuma kula da gidajen marayu.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.