BBC navigation

Ra'ayi Riga: Rikici Tsakanin Manoma da Makiyaya

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:42 GMT

Garmaho

A daidai wannan lokaci na shekara ne dai a kan samu rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma. Lokacin da manoma ke kokarin kwashe amfanin gonarsu bayan karashewar damuna, Fulani kuma na neman wuraren da za su ciyar da dabbobinsu.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

shanu

A wasu lokuta shanu kan cinye amfanin gona

A kusan dukanin lokaci makamancin wannan na shekara dai a kasashen yammacin Afrika ana samun matsalar fadan Fulani makiyaya da Manoma.

Hakan na faruwa ne kuwa bayan da damuna ta kare manoma ke kokarin kwashe amfanin gonarsu, manoma kuma na neman abincin da za su ciyar da dabbobinsu.

Dalilai da yawa ne dai kan haddasa wannan arangama da kusan ta zama ruwan dare, wadanda suka hada da rashin burtaloli da labi - labi da makiyayan za su bi da dabbobinsu domin kai wa wuraren kiyo.

A cikin yan kwanakin nan dai ana ta samun arangamar ta Fulani da manoma a wurare daban daban kama daga Nijar da Ghana da Kamaru da ma Najeriya.

Hakan kuwa ya biyo bayan cewar tuni wasu Makiyayan sun saki dabbobinsu, duk kau da cewa a wurare da dama ba'a ida aikin gonaki ba. Wannan dauki ba dadi na Fulani da manoma dai kan hadassa asarar rayuka da dukiya mai dama.

To shin me ke kawo wannan matsala ne, me kuma ya kamata a yi domin shawo kan lamarin? wadannan da ma sauran batutuwa ne za mu tattauna a filin namu na Ra'ayi Riga.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.