BBC navigation

Labarin Eastleigh, Kenya, cikin hotuna

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:37 GMT

Labarin Eastleigh, Kenya, cikin hotuna

 • Kare na bin masu zanga-zanga
  Wani dan sanda na amfani da kare wajen tarwatsa masu zanga-zanga a rana ta biyu da aka yi taho-mu-gama a unguwar Eastleigh
 • Matasa na jifa da duwatsu
  Wasu matasa 'yan Somaliya suna jifa da duwatsu a kan hanyar unguwar Eastleigh da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya
 • Wata mata tana tserewa
  Wata mata na gudu bayan ta jefa wa 'yan sanda duwatsu lokacin zanga-zangar
 • Masu zanga-zanga rike da makamai
  'Yan asalin kabilar Somali rike da makamai a lokacin da suke yiwa abokan gabar su ihu
 • Dan sanda na bin wani da gudu
  Wani dan sanda na kokarin kama wani mutum da aka samu yana sata a gidajen 'yan asalin kabilar Somali a rana ta biyu
 • Wasu Somaliyawa rike da kayansu suna kokarin barin gidajen su saboda rikicin
 • Motar da aka sanayawa bom a Nairobi
  Inda aka tashi bom a wata motar safa a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, al'amarin da ya haddasa zanga-zangar
 • 'Yan sanda rike da karnuka suna bin masu zanga-zanga
  'Yan sanda na amfani da karnukan da suka samu horo wajen tarwatsa masu zanga-zanga a rana ta biyu da aka yi taho-mu-gama a unguwar Eastleigh
 • Karnuka sun rutsa wani mutum
  Karnuka sun rutsa wani mutum da ya yi sata a gidajen 'yan Somaliya a rana ta biyu da aka yi taho-mu-gama a unguwar Eastleigh da ke Nairobin Kenya a ranar 19 ga watan Nuwamban shekarar 2012.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.