BBC navigation

Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:41 GMT

Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai

 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  A rana ta biyu a jere, masu sana'ar samar da madara sun taru a kusa da ginin Majalisar dokokin Tarayyar Turai a birnin Brussels domin zanga-zanga kan farashin madara.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  A ranar Litinin, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yiwa 'yan sandan da ke gadin ganin wanka da madara.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  An kuma kona wata mota dauke da mutum-mutumin wani manomi a gaban ginin Majalisar.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  Masu sana'ar madar sun ce faduwar farashin yana sanya da dama daga cikinsu kasa ci gaba da wannan sana'a.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  A daidai lokacin da aka shiga rana ta biyu, an rufe wasu daga cikin hanyoyin birnin, inda wasu jami'an Tarayyar Turan suka kasa halattar ofisoshinsu saboda manyan motocin da aka gindaya a kan hanya.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka fito daga kasashen Tarayyar daban-daban, sun rinka tashin hayaki a kan ginin.
 • Zanga-zangar masu sana'ar madara a Turai
  Masu sana'ar madarar sun ce suna bukatar karin kashi 25 cikin dari domin farfadowa daga asarar da suka yi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.