Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Mene ne fatan ku game da sabuwar shekara?

ambaliyar ruwa a Kebbi
Image caption Najeriya ta yi fama da ambaliyar ruwa a shekara ta 2012

Nan da kwanaki hudu masu zuwa ne za a shiga sabuwar shekarar miladiya wato shekara ta 2013.

Kowacce shekara dai kan zo da irin ta ta albarkar da kuma irin kalubalen da jama'a ko kasa kan fuskanta.

Tun daga farkon shekara ta 2012 ya zuwa yanzu, abubuwa da dama sun faru, wasu daga ciki ana murnar faruwarsu, wasu kuma ana juyayin afkuwarsu.

Ga kasa ko al'umma da zarar shekara ta kare, a kan dora fata a kan shekara mai kamawa musamman ma idan shekarar mai karewa an fuskanci matsaloli a cikinta.

To ko yaya shekara ta 2012 ta kasance mu ku, kuma mene ne fatanku game da sabuwar shekara mai kamawa?