Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Farfado da sufurin jiragen kasa a Najeriya

A Watan Disambar shekarar 2012 ne hukumar jiragen kasa ta Nigeria ta farfado da sufurin jirgin kasa tsakanin Jihar Lagos da kuma Kano.

Farfado da sufurin dai na zuwa ne bayan da aka shafe shekaru da dama da dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa a kasar.

A halin yanzu a kowane mako jirgin na zirga-zirga tsakanin jihohin Lagos a kudanci da Kuma Kano dake arewacin kasar sau daya.

Sai dai wasu da suka hau jirgin sun yi korafin rashin tsafta musamman ma a bandakunan jirgin.

Amma duk da haka wasu na ganin sufurin jirgin, zai taimaka wajen farfado da sufurin jiragen kasa a Nigeria da aka yi watsi da shi shekaru da dama.