Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Shirin rarraba wayoyin salula ga manoma a Najeriya

Wani manomi a Najeriya
Image caption Yawancin manoma a Najeriya na amfani da dabarun gargajiya ne a sana'arsu

A Najeriya, a farkon watan nan ne aka ambaci babban sakataren ma'aikatar ayyukan noma ta kasa, Ibukun Odusote yana cewar gwamnatin kasar ta kammala wani shiri na samar da wayar salula kyauta ga manoma miliyan goma a yankuna karkara.

Mr Odusote ya ce hakan zai ba ma'aikatarsu damar ilmantar da manoman da kuma tuntubar su, duk dai a yunkurin bullo da zamananci a ayyukan noman a Nijeriya.

To sai dai shirin na shan suka daga bangarori da dama, inda wasu ke korafin cewa ba abin da manoman karkara suka fi bukata ba kenan.