Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

CAF 2013: Tawagar Nijar ta isa Afrika ta Kudu

Tawagar jamhuriyar Nijar ta isa kasar Afrika ta Kudu domin fafatawa a gasar cin kofin kasashen Afrika. Wannan bidiyon ya nuna 'yan wasan suna atiyasi a gabar wani teku.

'Yan wasan da masu horas da su sun ce sun shirya tsaf domin fuskantar gasar, inda za su fafata a rukuni B da kasashen Ghana da Mali da kuma DR Congo.