Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Auren cin kasuwa a Nijar

Jonathan da Muhamadou Issoufou
Image caption Nijar da Najeriya kasashe ne makotanjuna

A jamhuriyar Nijar wasu iyaye na aurar da 'yan mata, musamman 'yan kabilar Abzinawa ga wasu mutane ta hanyar dillalai a kai su Najeriya.

Kuma a mafi yawancin lokuta 'yan matan basu san mazajen ba.

Hakan dai ba karamar matsala ya ke haddasa wa ba, kasancewar ana aurar da 'yan matan ne masu shekaru sha daya zuwa sha biyar da haihuwa.

Kuma ana cire su ne daga makaranta don a yi masu auren.

Gundumar Tanut dake jahar Damagaram na daya daga cikin yankunan da wannan al'ammari ya ke dada yawaita.

Wakiliyar BBC ta ziyarci garin na Tanut don gane ma idanunta halin da ake ciki game da irin wannan aure da ake kira na cin kasuwa.