Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ko me ya sa kasashen waje ke katsalandan a Afrika?

Sojojin Faransa a Mali
Image caption Faransa za ta tura sojoji 2000 ne zuwa Mali

Tawaye a ƙasashen Afurka dai abu ne da aka daɗe ana ganinsa tun daga lokacin da turawan mulkin mallaka suka shigo nahiyar.

Sai dai a wancan lokacin, turawan na ɗaukar hanyoyin murƙushe 'yan tawayen ba tare da wata- wata ba.

To bayan samun 'yancin kai kuma, batun tawaye bai sauya zane ba a nahiyar Afurka domin kuwa gwamnatocin ƙasashen nahiyar da dama na fama da wannan matsala, inda a yawancin lokuta 'yan tawayen kan yi kokarin kifar da gwamnatin ƙasarsu.

Sai a yunkurinsu na murƙushe 'yan tawayen, gwamnatocin ƙasashen na neman ɗauki daga waje, duk da cewa suna da rundunonin soja na kansu.

Misali a nan shi ne, abinda ke faruwa yanzu haka a ƙasar Mali. A can baya kuma a ƙasashe kamar Sudan da Liberia da Saliyo da dai sauransu, an samu irin haka.

To ko me ya sa kasashen da suka fuskanci tawaye ba sa iya shawo kan matsalar da kansu? Kuma mece ce illar shigar dakarun kasashen waje wajen shawo kan matsalar tawaye a kasashen Afrika?