Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kula da Cutar Sankara

Cutar sankarar
Image caption Cutar sankarar huhu ta fi kama maza

Mutane na fadawa hadarin kamuwa da cutar sankara, idan sun fara manyanta.

Haka kuma shan taba na lalata sinadaran dake jikinmu ko tururin matsanancin zafin rana.

Duk shekara a fadin duniya ana samun sabbin nau'oin sankara kimanin miliyan 13.

Ba wai matsala ce da ta tsaya kawai ga kasashen da suka cigaba ba, domin kusan rabin wannan ciwo ana samunsa ne a kasashen dake tasowa.

Maza sun fi fama da cutar sankarar huhu, yayin da mata kuma suka fi fama da cutar sankarar mama. 35