Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dama shugaban kasar Ghana ya iya Hausa?

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya bayyana matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka na tura sojojinta zuwa kasar ta Mali a matsayin abin daya dace.

A ranar Litinin ne rukunin farko na sojojin kasar sama da 120 suka tashi daga filin saukar jiragen saman birnin Accra.

Komla Dumor na sashen talabijin na BBC Focus on Africa, ya tambayi shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama, ko yaya yake kallon rikicin kasar ta Mali ?