Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sojojin Mali na bincike gida-gida a Gao

Sojojin Faransa a Gao
Image caption Dan kunar bakin wake ya kai hari a Gao, shi ne na farko tun da dakarun Faransa suka fara jagorantar na Afrika, wajen fatattakar masu fafutukar Islama a Mali

A kasar Mali, dakarun gwamnati na bincike gida-gida, domin gano masu fafutukar Islama, biyo bayan harin ba zata da suka kai a Gao dake arewacin kasar a ranar Lahadin data gabata.

An fattaki 'yan tawayen makonni biyu da suka wuce, amma yayin da rahotanni ke cewa sojoji sun karbe iko da garin, mazauna garin na cikin fargaba matuka.