Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Makanta ba ta hana Cobhams zama tauraro ba

Cobhams Asuquo na daya daga cikin masu tsara wakoki da ake ji da su a Afrika, hakan ya biyo bayan iya sarrafa na'ura da kayan kida a fagen wakokin zamani a Najeriya.

Tun yana karami kusan yana iya kida da komai, kama daga teburin cin abinci da kayan girki da kida da kirjinsa da cikinsa da kuma yin fito.