Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya : Hira da Mallam Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau
Image caption Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau

A Najeriya manyan jam'iyyun adawa na ACN da ANPP da CPC da kuma APGA, sun bayyana shirinsu na hadewa domin kafa sabuwar jam'iyyar adawa ta APC.

Sabuwar jam'iyyar dai za ta kalubalanci jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

A baya dai jam'iyyun adawar sun yi irin wannan yunkuri, amma bai ci nasara ba.

Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ANPP a zaben shekara ta 2011, shi ne ke wakiltar jam'iyyarsa a yunkurin hadakar da ake yi.

Yayin da ya kawo ziyara BBC, Naziru Mikail ya tattauna da shi game da wannan batu, inda ya fara da tambayarsa, shin ko ta yaya wannan hadaka za ta yi aiki?