Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Ko wane hali Gwamnan jihar Taraba ke ciki?

Hatsarin jiragen sama ba sabon abu bane a Najeriya
Image caption Hatsarin jiragen sama ba sabon abu bane a Najeriya

A Najeriya, jihar Taraba na fuskantar tangal-tangal ta fuskar siyasa da zamantakewa, biyo bayan hatsarin da gwamnan jihar Danbaba Danfulani Suntai ya yi.

Gwamnan ya yi hatsarin a jirgin sama, a watan Oktobar bara, inda ya samu munanan raunuka da suka sanya aka garzaya dashi kasar Jamus domin kula da lafiyarsa.

Daga bisani kuma aka rantsar da mataimakinsa, Alhaji Garba Umar a matsayin mukaddashin gwamna, a cikin watan Nuwambar bara.

Kawo yanzu ba a ga gwamnan ko jin muryarsa a bainar jama'a ba, abin da ya haifar da rahotannin dake cewa, ya nakasa ba zai iya cigaba da gudanar da mulkin jihar ba.

A filin Gane Mani Hanya na wannan mako, wakilinmu Is'haq Khalid ya tattauna da gwamnan jihar na riko, Alhaji Garba Umar, kan halin da gwamnan jihar Danbaba Suntai ke ciki.

Haka kuma sun tabo rikice-rikicen da jihar ke fuskanta, amma wakilin namu ya fara ne da tambayarsa ko shin ya yake kallon hawansa kan kujerar gwamna, a cikin makwanni uku kacal daga matsayinsa na dan kasuwa?