An nemi a baiwa 'yan tawayen Syria makamai

Image caption Shugaban Burtaniya David Cameron da na Faransa Fracios Hollande

A yayin da aka shiga shekara biyu ana rikici Syria, Faransa da Burtaniya na neman a dage takunkumin shiga da makamai kasar domin tallafawa 'yan tawaye.

Shugaban Burtaniya David Cameron da na Faransa Francios Hollande sun ce za su baki a taron shugabanin kasashen Turai da ake yi a Brusells domin ganin a dage takunkumin da aka sanyawa Syria na shigo da makamai.

Shugabanin kasashen biyu dai sun ce suna son su taimakawa 'yan tawayen ne a yakin da suke yi da gwamnatin Shugaba Assad.

Amma dai kasashen Turai da dama basu amince da hakan ba.

Francois Hollande ya nuna karara cewa yana son tarrayar Turai ta dage takunkumi makamai da ta kakkabawa Syria.

Faransa wadda take ra'ayi daya da Burtaniya ta yi zargin cewa kasashen Iran da Rasha na ci gaba da taimakawa gwamnatin Syria da makamai kuma a ganinsu taimakawa 'yan tawaye da makamai ne zai karawa gwamnatin shugaba Assad matsin lamba.

Jami'an kasar Burtaniya sun ce a yayinda aka shiga shekara biyu ana rikicin na Syria, wanda ya yi sanadiyar mutumar sama da mutane dubu saba'in dolene a sake waiwayar batun shigo da makamai a kasar.

Pira Ministan Burtaniya ya ce kasar na shirin janye goyon bayan da take bayarwa akan takunkumi shigo da makamai a Syrian.

Faransa ma tabi sahun Burtaniya ne a kan wanna batun kuma ta ce za ta shiga gaba-gaba a kokarin ganin an yi hakan.

Kasashen biyu dai na kokarin ganin sun shawo kan sauran kasashen Turai, kamarsu Jamus da Sweden da kuma Austrailia wadanda suke nuna shakku game da batun.

A watan Mayu ne dai za'a sake sabonta takunkumin, amma idan ba'a samu hadin kai tsakanin kasashen Turai ba, kasar Faransa da Burtaniya ba za su amince a sake sanya takunkumin ba.