Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mai zai faru idan kowa na da mota?

Akwai motoci fiye da biliyan daya a duniya yanzu - kuma nan da shekara ta 2050, za su iya kaiwa biliyan hudu, a daidai lokacin da masu matsakaicin hali a kasashe kamar India, China da Brazil ke kara mallakar motoci.

Sai dai idan mutane da dama na son tuka mota - ta yaya za a kaucewa cunkoso?

A wani bangare na shirin BBC 'Hangen rayuwa ta gaba a duniyar ka' mun duba yadda fasaha za ta taimaka wurin ganin an rage cunkoso a daidai lokacin da mutane ke kara mallakar motoci.