Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Kimiyya a Afrika

Shirinmu na gane mini hanya na wannan makon zai duba batun ilimin kimiyya ne a nahiyar Africa.

Ranar Alhamis din da ta wuce ne aka kawo karshen wani da sashen BBC mai watsa shirye-shirye zuwa kasashen waje, watau BBC World Service ya shirya a Kampala babban birnin kasar Uganda.

A taron, Masana ilimin kimiyya, musamman daga kasashen africa ne suka kwashe mako guda inda suka yi mahawara akan rawar da Africa ke takawa a fannin kimiyya.

Daya daga cikin wadanda suka halarci taron sjhine Malam Sarki Adamu Musa, wanda ke Jami'ar Kampala International University da ke Ugandar.

Bayan da aka kammala taron, Aishatu Musa ta tuntube shi domin jin ko Africa zata iya zama jagora a fannin kimiyya?