Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da janar Muhammadu Buhari mai ritaya

Jagoran jam'iyyar adawa ta CPC a Najeriya, Janar Muhammadu Buhari ya ce, yanzu 'yan Najeriya sun ji a jikinsu, kuma hada kan da 'yan adawa suka yi shi ne kawai mafita ga kasar.

Buhari ya kuma ce, dukkan 'yan adawa a Najeriya sun koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya.

Dangane da batun tsaro kuma Janar Buhari yace, alhakin kare rayuka da dukiyar jama'a ya rataya ne a wuyan gwamnati.

Janar ya kuma koka a kan yadda cin hanci da rashawa ke sake habaka a Najeriya, kuma lokaci yayi da jama'a zasu samar wa kansu shugabanci nagari ta hanyar da tsarin dimokradiyya ya samar musu.

Janar Buharin ya ziyarci BBC kuma a hirarsa da Isa Sanusi, ya soma ne da yin tsokaci a kan matsalar tsaro a Najeriya.