Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ahuwa ga kungiyar Boko Haram

Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

Ranar Larabar nan ce Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da kafa wani kwamiti mai wakilai 26 da zai sasanta da kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid da'awati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram .

Hakan ya biyo bayan nazarin da Majalisar tsaron Nigeria ta yi ne akan wani rahoto da aka gabatar wa shugaban a kan batun yi wa 'yan kungiyar ta Boko Haram ahuwa.

Sai dai kafin bada sanarwar kafa kwamitin, kungiyar ta yi watsi da matakin tana cewa, ita ce ma ya kamata a nemi afuwa daga gare ta, saboda laifukkan da take zargi an aikata ma ta.

To yaya kuke ganin wannan mataki, wane tasiri zai yi, kuma ta yaya za a bullo ma wannan al'amari? Wasu kenan daga cikin batutuwan da za mu tattauna kan su a filinmu na Ra'ayi Riga na yau.