Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shin me ya janyo kashe kashe a garin Baga

Image caption Gidajen da suka kone a Baga

A Najeriya wani batu dake janyo kace-nace shi ne tashin hankalin da aka yi a garin Baga na jihar Borno tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Rahotanni na cewa, mutane sama da 185 aka kashe, da mata da kananan yara.

Amma rundunar sojan Najeriya tace, mutane 37 suka mutu. Ko me ya kawo jinkiri wajen bayyanar labarin abinda ya auku a Baga?

Shin yaya za'a tantance gaskiyar ta'asar da ake zargin an aikata a garin Baga?

Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna filin Ra'ayi Riga na wannan makon.