Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sabon arzikin Ghana

Sama da shekara biyu ke nan tun bayan da Ghana ta fara hako man fetur don sayarwa a rijiyoyin man da ke cikin teku. Gwamnati na da kwarin gwiwa cewa man zai bunkasa tattalin arzikin kasar. Don haka ta karbo makudan kudade bashi da nufin gina sababbin ababen more rayuwa. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, shekaru biyu baya wanne alfanu man ya yi ga al'ummun Ghana wadanda suka fi kusanci da shi--wato al'ummar birnin Takoradi mai tashar jiragen ruwa?