Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Dokar ta baci a jihohin arewa uku

Image caption Sojojin Najeriya

Tun bayan da Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa na arewacin, mutane daga sassa daban-daban na kasar ke tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan mataki.

Yayin da wasu ke na'am da matakin,wasu kuwa suna nuna rashin amincewa ne . A jawabinsa a gidan talabijin na kasar a ranar Talatar data wuce, Shugaba Jonathan ya ce sojoji za su dauki dukkan matakan da suka dace don kawo karshen masu rike da makamai tare da samarda tsaron dukiya da kuma al'umma.

Tuni dai, kakakin shalkwatar tsaron Najeriya, Brigadier Janar Chris Olukolade ya ce sun soma luguden wuta a kan sansanonin 'yan kungiyar Jama'atu AhlusSunna Lid'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram.

A cewar rundunar sojin Najeriyar , a kwana 2 jere tayi amfani da jiragen yaki da kuma helikoptoci na kai hari a gandun dajin Sambisa dake kudancin jihar Borno, inda ake ganin cewar gandun dajin ya kasance wata matattara ta 'yan boko haram.

To ko tura karin dakarun zuwa wadanan jihohi zai kawo karshen zubar da jinin da ake yi , kuma shin ko sojojin za su gudanar da ayyukansu ba tare da keta hakkin jama'ar da ba su ji ba su gani a wadannan yankuna, kamar yadda aka yi ta zargin suna yi tun farko ba?