Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kade-kaden Afirka: Mokoomba daga Zimbabwe

Matasa shidan da suka hadu suka yi Mokoomba sun sha gwagwarmaya.

Sun fito ne daga kabilar Tonga maras rinjaye, kuma ba kowa ne ke fahimtar harshen da suke wakokinsu da shi ba, hatta a Zimbabwe.

Amma sun dage sai sun kai labari a matsayinsu na mawaka, kuma sun kai din.

A shekaru biyun da suka gabata kuma sun bayyana a matakin kasa-da-kasa, inda kuruciyarsu da azancinsu, da takun rawarsu suka kayatar da 'yan kallo.

An bayyana album din Mokoomba na biyu, wanda aka saki a 2012, a matsayin "lamba daya a tsakanin sababbin album-album daga wata kungiya da ba a santa ba"*.

Sautin wakokin Mokoomba ya yi kama da na zamani, duk da cewa suna samo asali daga wake-waken gargajiya na Tonga. 'Ya'yan kungiyar na matukar sha'awar ganin al'adunsu sun shahara a duniya.

*A cewar Afropop Worldwide, Amurka