Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar barnata abinci

Image caption Yadda ake ɓarnata abinci

Wani bincike na hukumar abinci da aikin gona ta majalisar dinkin duniya yace, a duk shekara ana barnatar da abinci tan 1.3 biliyan a duniya.

Kuma wasu masana na cewa, wannan yana daya daga cikin dalilan dake haddasa yunwa a duniya.

Ko yaya matsalar take a yankunanku? Kuma me manoma ke bukata domin kaucewa lalacewar amfanin da suka noma?

Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a filin Ra'ayi Riga na yau.