Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Apple ya yi gyara a wayar iPhone

Kamfanin lataroni na Apple ya bayyana gyaran da ya yi mafi girma tun lokacin da ya kaddamar da wayar komai da ruwanka ta Iphone a shekarar 2007.

Sabuwar masarrafar ta IOS 7 ta kunshi manhajar samun wakoki kyauta na iRadio da sauransu.

Haka kuma akwai wani sauyi na ban mamaki a naurar Mac pro.

Apple ya kuma sanar da sauyi a masarrafar kwamfutar kan tebur na OS Ten Mavericks.

Dukkanin masu samar da manhajoji ga Apple na da wadannan gyare-gyare, kafin masu wayoyin su amfana da su a watanni uku zuwa hudu masu zuwa.