Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Hira da Sule Lamido

Image caption Alhaji Sule Lamido

Jam'iyyar PDP mai jan ragamar mulki a Nigeria na fuskantar matsaloli da dama, inda wasu ke kira ga shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur da yayi murabus.

Hakan dai ya biyo bayan takaddamar da ta shiga tsakanin gwamnoni ne a lokacin zaben shugaban kungiyar gwamnoni ta kasa wataU Governors Forum.

Ko menene ke haddasa wadannan rigingimu kuma yaya za a warware su, wasu kenan daga cikin tambayoyin da Alhaji Sule Lamido, gwamnan jihar jigawa ya amsa a shirinmu na gane mini hanya.