Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan gudun hijiran Mali na tsoron komawa

Watanni biyar kenan da dakarun sojin Faransa suka shiga cikin rikicin Mali, sai dai har yanzu wasu daga cikin mutanen da suka yi gudun hijira na dari-darin komawa gida.

Duk da cewa akwai ragowar sojoji 3,000 na Faransa a yankin, izuwa yanzu sojojin sun samu nasara.

A yanzu haka ana kokari ne dan ganin an tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da shirye-shiryen yin zaben shugaban kasa a karshen watan gobe.