Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Rikicin cikin gida a PDP

A Najeriya, jamiyyar PDP na mulkin kasar tun shekarar 1991, sai dai a yayin da zaben shekara ta 2015 ke karatowa, jam'iyyar na fuskantar matsalolin cikin gida.

Lamarin da wasu daga cikin 'ya'yanta da kuma 'yan adawa ke ganin tamkar jam'iyyar ta samu nakasu ne.

Rikicin da jam'iyyar ke fama da shi ya dada fitowa fili ne, bayan da aka yi zaben Kungiyar Gwamnonin kasar a watan Mayun da ya gabata.

Inda kungiyar ta rabu gida biyu tsakanin wadanda ake musu kallon suna tare da Shugaban kasa Goodluck Jonathan, da kuma wadanda ake ganin ba sa tare da shi.

Masana harkokin siyasa na cewa Shugaban kasar na son samun iko ne kan gwamnonin, saboda takarar zaben shekarar 2015, duk da cewa bai furta a zahiri cewa zai fito takarar ba.