Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rikicin siyasar kasar Masar

Image caption Magoya bayan Mohammed Morsi

Yanzu dai rikicin siyasar kasar Masar ya dauki wani sabon salo, bayan da sojoji suka soke kundin tsarin mulki, suka kuma nada babban Alkalin kasar a matsayin shugaban riko, kafin sabbin zabubuka.

Lamarin ya biyo bayan zanga zangar nuna adawa da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi ne da aka kwashe kwana da kwanaki ana yi.

To ko me wannan yake nufi ga dimokradiyyar Masar din? Kuma yaya makomar kasar za ta kasance?